Magana Jari ce Littafi Na Uku : Part 3 of 3

Contains Ads

Magana Jari ce Littafi Na Uku : Part 3 of 3

Karanta Littafin Magana Jarice Na Uku. Magana Jarice Part 3 of 3

Karanta cikakken littafin magana Jarice littafi na uku. Magana Jari ce littafi na uku wallafar Alhaji Dr. Abubakar Imam kamfanin Gaskiya Zaria.

Wannan littafi, `Magana Jari ce, 3', yana cikin littattafai guda uku da Alhaji Abubakar Imam ya rubuta a cikin wata shida na zamansa a Zariya a shekarar 1936. Dalilin za6o shi kuwa ya rubuta wadannan littattafai shi ne ya shiga wata gasa to rubutun littafi a shekarar 1933 ya kuma ci nasara da littafinsa na farko 'Ruwan Bagaja'.

MAGANA JARICE LITTAFI NA UKU - Yaro Bada Kudi A Gaya Maka!

A cikin wannan manhajja akwai cikakkun labaru kamar haka:

☆ Magana Jari Ce

☆ Kowa Ya Dogara Ga Allah Kada Ya Ji Tsoron Mahassada, Balle keta

☆ In Allah Ya Taimake Ka, Kai Kuma Taimaki Na Baya Gareka

☆ Girman Kai Rawanin tsiya

☆ Wanda Ke Wulakanta Jama.a Duk Ya Ga Iyakarsa

☆ Mara Gaskiya Ko Cikin Ruwa Yayi Jibi

☆ Dan Hakin Daka Raina Shi Ke Tsone Ma Ido

☆ Alheri Danko Ne, Ba Ya Faduwa Kasa Banza

☆ Munafunci Dodo, Ya Kan Ci Mai Shi

☆ Kwadayi Mabudin Wahala, Im Ba Kwadayi, Ba Wulakanci

☆ Yaro Bata Hankalin Dare Ka Yi Suna

☆ Karen Bana Shi Ke Maganin Zomon Bana

☆ In Zaka Gina Ramin Mugunta, Gina Shi Gajere

☆ Rama Cuta Ga Macuci Ibada

☆ Mai Arziki Ko a Kwara Ya Sai Da Ruwa

☆ Labarin Sarki Jatau

☆ Sa'a Wadda Ta Fi Manyan Kaya

☆ Hassada Ga Mai Rabo Taki

☆ Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara, Ko Ana Muzuru Ana Shaho Sai Ya Yi

☆ Mai Rabon Shan Duka Ba Ya Jin Kwabo, Sai Ya Sha

☆ Labarin Sususu Da Shashasha

☆ Kowa Ya Daka Rawan Wani, Ya Rasa Turmin Daka Tasa

☆ Sai Bango Ya Tsage, Kadangare Ke Samun Wurin Tsiga


An haifi Alhaji Dr. Abubakar Imam, O.B.E; C.O.N.; LL.D (Hon.) N.N.M.C. a shekarar 1911 a cikin garin kagara sa'an nan tana cikin lardin Kwantagora, yanzu kuwa Jihar Neja. Ya Yi makaranta a Katsina Training College kuma ya kama aikin malanta a Makarantar Midil to Katsina a shekarar 1932. Yana da shekara 22 ya rubuta `Ruwan Bagaja'. Ganin kwazonsa wajen Raga labari mai ma'ana ya sa Dr. R.M. East shugaban Offishin Talifi na Zariya ya roki a ba da shi aro daga Katsina ya yi aikin rubuce rubuce a Zariya. Bayan ya koma Katsina aka bi shi da rokon ya kara rubuta wasu , littattafan. A can ya rubuta 'Karamin Sani kukumi' cikin 1937. A cikin shekara 1938 sai Gwamnan Kaduna ya roka a dawo da Imam Zariya a koya mashi aikin edita ya zama editan jaridar farko to Arewa. Shi ne ma ya rada mata suna `Gaskiya Ta Fi Kwabo' aka fara bugawa a watan Janairu na shekara 1939.

Ya yi shekara 12 yana wannan aiki na edita har ma ya rubuta wani littafi a lokacin `Yakin Duniya Na Biyu' watau `Yakin Hitila' da ya ba suna `Tafiya Mabudin Ilmi'. Wannan littafi ya ba da Iabarin tafiyarsa tare da wasu editoci na jaridun Africa to Yamma zuwa Ingila a jirgin ruwa a shekara 1943.

Akwai sauran littattafa masu zuwa irinsu:

- Magana Jari

- Littattafan Hausa

- Tarihin Annabi Kammalalle wallafar Alhaji Dr. Abubakar Imam

- Littafin Magana Jarice part 1

- Ruwan Bagaja

- Iliya Dan Mai Karfi

- Zaman Mutum Da Sana'arsa

- Magana Jari ce littafi na uku

- Magana Jarice yaro bada kudi a fada maka

- Abubakar Imam Memoirs

- Littafin Magana Jarice na daya

- Littafin magana jarice audio

Da dai sauransu in shaa Allahu.

Idan kunji dadin wannan manhajja ta magana jarice 3, sai ku ba manhajjar tauraro biyar, ku rubuta tsokacinku kuma sannan ku aikata zuwa ga yanuwa da abokai.

Domin samun littafin magana jari ce part 1 da kuma magana jari ce part 2 sai ku duba sauran manhajjoji na team abyadapps cikin wannan gida.

Idan akwai wata shawara ko tsokaci, sai ku aiko mana da sako a adireshinmu wato abyadapps@gmail.com. In shaa Allahu zamu karanta mu aiko muku da amsa.


MAGANA JARI CE PART 3 of 3.
Read more
Collapse
4.8
87 total
5
4
3
2
1
Loading...

What's New

Mun saka shafuka 166 zuwa 170 wato labarin mai arziki ko a Kwara ya sai da ruwa an cika shi.
Sannan labarin kowa ya daka rawar wani...shima mun gyara matsalar yanzu labarin an kammalashi.

Please update your app and enjoy.
Read more
Collapse

Additional Information

Updated
October 2, 2018
Size
54M
Installs
10,000+
Current Version
3
Requires Android
4.1 and up
Content Rating
Everyone
Permissions
Offered By
Abyadapps
©2019 GoogleSite Terms of ServicePrivacyDevelopersArtistsAbout Google|Location: United StatesLanguage: English (United States)
By purchasing this item, you are transacting with Google Payments and agreeing to the Google Payments Terms of Service and Privacy Notice.