Aikin Hajji, daya ne daga cikin shikashikan Musulunci biyar, da ake wajabta wa Musulmai masu hali su yi ko da sau daya ne a rayuwarsu. Ana gudanar da aikin Hajji ne a kwanaki biyar wanda ake farawa daga 8 ga Zul Hajji zuwa 12 ko 13 ga watan. A Duk shekara kimanin miliyoyin mutane ne ke gudanar da aikin Hajji a Saudiyya, wanda shi ne taro mafi girma a duniya.
Wanna Manhaja anyi shi ne domin sauki ga Maniyyatan Aikin Hajji ga Al-Ummar Musulmi baki daya a dukkanin fadin duniya a harshen hausa.
Wannan App yana haskakawa Mahajjata yadda zasuyi aikin hajjin a sunnan ce yayinda suke aikin su na hajji ba tareda sun samu wata wahala ba. Dalili kuwa shi ne zakaga an samu mantuwa ko rashin sani ko bukatar tambaya, da wannan ne mukaga ya kamata a fitarwa al-umarmu hausawa kuma musulmi yadda zaiyi amfanida salularsa (wato Handset) ya saukar da wannan manhaja (Application) domin samun saukin Aikin Hajji a saukake.
Allah Ubangiji ya bamu ladar wannan aikin. Amin