Assalamu Alaikum,
Barka da zuwa Bugun Kasa 7, sabuwar manhaja (Application) da aka kirkira domin saukaka muku harkar lissafin Bugun Kasa da Ramli. Wannan manhaja tana taimakawa wajen yin lissafi cikin sauri da sauki ba tare da dogon rubutu ko shan wahala ba.
Abubuwan da wannan manhaja ta kunsa sun hada da:
Lissafi Mai Sauki: Tana fitar da dukkan siffofin da suka dace a take.
Jadawalin Kasa: Bayani dalla-dalla akan yadda abubuwan suke tafiya.
Bincike na Musamman: Tana taimakawa wajen duba lamura daban-daban kamar:
Neman Aure
Neman Sa'a
Hanyar Tafiya
Da sauran al'amuran yau da kullum.
Adana Tarihi (History): Za ka iya ajiye (Save) duk aikin da ka yi don dubawa anjima.
Full Read: Samun cikakken bayani a waje daya.
Interface Mai Kyau: An tsara ta yadda kowa zai iya amfani da ita cikin sauki, ko da baka taba amfani da irinta ba.
Wannan application kyauta ne domin kowa ya amfana. Sauke Bugun Kasa 7 yanzu domin samun ilimi da saukin bincike a tafin hannunku.
Mungode da zabar wannan manhaja!