Curious Reader Parents na kawo wasannin koyon-karatu-a-matankin-farko kyauta ga kowace waya — bai buƙatar yanar gizo/data (bayan saitin shi a karon farko), ba'a buƙatar asusun manhaja, ba'a buƙatar wasu bayanai yayin buɗewa.
Ƙungiya mai zaman kanta ta Curious Learning ce ta ƙirƙiri Curious Reader Parents, wanda dandali ne da ya ƙunshi hanyoyin koyo guda biyu:
Ciyar Da Dodo (Feed The Monster) — Wasan koyon furuci cikin nishaɗi wanda ke koyar da sautukan haruffa da kuma yadda ake haɗa su don bada ma'ana.
Littattafai Masu Murya (Interactive Books) — wani zauren karatu mai dauke da tarin littattafai masu hotuna waɗanda yara zasu iya karantawa (da kuma sauraro) da kansu.
Dukansu suna samuwa a tarin yaruka daban-daban da kuma nau'ikan fakitin yare daban-daban, sa'an nan kuma ana cigaba da ƙara wasu akai-akai — ba tare da buƙatar sabunta manhajar ba.
An tsara manhajar ne don amfanin yau da kullum, ba kawai don ɗan gwaji akan Wi-Fi ba.
Tana aiki ba tare da yanar gizo/data ba. Bayan anyi saitin ta sau ɗaya da farko, kowane wasa da kowane littafi suna aiki ne gaba ɗaya ba tare da yanar gizo/data ba — Wannan ya dace ƙwarai da gidaje da kuma ajujuwan da babu tabbataccen sabis ko datar waya.
Babu buƙatar asusun manhaja, babu buƙatar wasu bayanai yayin buɗewa, babu buƙatar kalmar ko lambobin sirri. Yaro zai iya fara wasa bayan 'yan danne-danne kaɗan, ba tare da wahalar yin wani saitin asusu ba.
An tsara manhajar domin iyaye suma. Allon kula da koyo na iyaye mai sauƙin amfani na nuna lokacin karatu a lissafin mako-mako, yana nuna iya nasara da akayi kan matakin koyo da ake son cinma, da kuma iya nisan da yaro yayi a kowane wasa, domin ku ringa ganin yadda yaranku suke koyo.
Babu sayan wani abu a cikin manhajar. Babu tallace-tallace kwata-kwata. Curious Reader Parents shiri ne na koyon karatu a kyauta, ba manhaja ce da tallace-tallace ke ɗaukar nauyinta ba.
Manufarmu: Ƙungiyar Curious Learning na aiki ne kawai domin saka ingantattun kayan koyon karatu da suka dogara kan sautukan haruffa, a hannun kowanne yaro dake faɗin duniya wanda bai iya karatu ba tukunna — musamman yaran da basu da ingantaccen sabis na yanar gizo, basu da damar zuwa makaranta, ko kuma basu da littattafai a gida. Curious Reader Parents itace hanyar da wannan shirin ke kaiwa har zuwa ga wayar da bata ma taɓa shiga yanar gizo, hawa online, ko samun data ba ma.
Samu ƙarin bayani a curiouslearning.org.
Wasanni da littattafai kyauta na koyon karatu, ba sai da intanet ba. Babu talla.